MENENE CIWON SANYI GABA (SYPHILIS)

 CIWON SANYIN GABA DA YADDA AKE MAGANCE SHI


CIWON SYPHILIS (CIWON SANYIN GABA)


ABDUL ADAMU SANI WUDIL


Ɗantaƙai Taccen Bayani Akan Ciwon Syphilis. Sakamakon Ciwone Me Hatsari Acikin Al'umma .


Wannan ciwon Yana Samuwane Sakamakon Kamuwa Da Wata Kwayar Hallitta Da Ake Kira Treponema Pallidium.

Tana Yaduwa Tahanyar Saduwa Tsakanin Mace Da Namiji ,Ko Kuma Mace Mecike Wacce Kedauke Daciwon Zata Iya Sawa Dan Da Yake Cikinta (congenital syphilis).

Karanta: matsalolin-inzali-da-hanyar-magance-su

Tana zama tsawon sati 2 zuwa 3 kafin tafara nuna alamominta ajikin mutum wato daga ranar da aka ɗauketa.


ALAMOMIN WANNAN CIWO.


Akwai zazzabi, wasu irin quraje pink color a jiki, ciwon gabobi, radadi da zafi a kwaroron gaban namiji dakuma gaban mace.

KarantaYADDA-AKE-RAGE-SHA'AWA

Wannan ciwo yana da hatsari sosai yakan rabuwa gida Uku primary syphilis da Secondary Syphilis and tertiary syphilis .


Ciwon Sanyi

Karanta: ABUBUWAN-DAKE-SA-YAWAN-MATUWA


YA ZA AMAGANCE WANNAN CIWON?


1. Ta hanyar yin test wato v d r test

2. Daina zinace zinace. takowanne yanayi.

3. Zuwa awu dan kula da lafiyar uwa data jaririnta.


DASAURANSU ALLAH YABAMU LAFIYA .DA ZARAR ANGA DAYA DAGA CIKIN ALAMOMINNAN TO AJE ASIBITI DA SAURI.HANYOYI 10 DA ZAKIBI DAN RABUWA DA KURAJEN PIMPLES

Menene Pimples ko Acne?
What Is a Pimples or Acne?
Pimples Wasu ƙuraje ne dake fitowa a fuskar Mutum Mace ko namiji, Basuda Girma Kuma suna tara ruwa fari amma basa yin Ɗiwa, suna da zafi idan aka matse su sukan ɗan kumbura kaɗan. Suna fitowa da yawa a fuskar mutum wasu kuma ba yawa ɗaɗɗaya yake fito musu ya danganci Halittar Mutum. Akwai Nau'in mutanen da basa yin Pimples ma Kwata kwata.

Causes of Pimples:
Abun dake Kawo Pimples:

Ya danganci Yanayin zubin Halittar mutum ne, Wasu Sunada Halittar Yin Pimples wasu kuma basuda shi. 

- Wasu Haka Kawai yake fito Musu.
- Wasu Kuma Yanayin Ƙarfin Sha'awa ce idan tayi Musu Yawa Suke sa Pimples Ya Fito a Fuskar Su.
- Wasu Kuma Idan Suka ci Gyaɗa ko Wani Abun ci Sai Pimples ya Fito Musu.
- Wasu Yanayin Ruwan Da Suke sha ko wanka dashi. Etc
- Wasu Kuma Cutace Ta Saɗaure, ko Sanyi Da Sauran su.


How to Get Rid of Pimples:
Hanyoyin da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’:

1. Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da ƙurajen pimples suke da yawa. Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin
man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rinƙa maimata hakan har zuwa waɗansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki.


2. Ki kasance mai yawan shan ruwa. Yana da kyau duk inda za ki je ki sanya ruwa a jikin jakarki ba wai dole sai kayan kwalliya ba. Yawanta shan ruwa ba wai zai
sanya miki laushin fata ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaƙi da ƙurajen pimples din da
suke fuskarki. Haka yana da kyau ki guji yawan cin abincin gwangwani, kasancewar suna dauke da wasu sinadarai da za su rika sanya ƙurajen fuska. Yakamata ki yawaita cin ƴaƴan itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da kankana da sauransu.


3. Ki rinƙa amfani da abin shafawar da ake kira ‘Antiodident spray’, irin su Jane Iradale da Neutrogenia Rapid Clear da Acne Eliminating Spot Gel da sauransu, hakan zai taimaka miki wajen daidaita man da ke fatarki, wanda masana fata suka ce idan ya yi yawa yakan haifar da ƙurajen fuska.

4. Ki kasance mai amfani da man ‘Cornmeal’ a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a hankali su bace.
Misalin man shi ne, Intagilo Clear Sal Cleanser. Sannan ki riƙa amfani da man da ke hana yaɗuwar ƙwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba ɗaya, sannan yana yaƙar ƙwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire miki Ƙwayoyin halittar da suka mutu a cikin fatarki. 
Misalinsu; Phytomer Gommage da Luffa-0.


5. Yana da kyau ki ware wata rana ko waɗansu ranaku a cikin mako ba tare da kin shafa kayan
kwalliya a fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar fuskarki samun ƴancin shigar da kuma fitar da iska ta ƙofofinta ba tare da wani cikas ba. Haka idan za ki shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to ki yi amfani da kayan kwalliyar da ba sa toshe ƙofofin fatar fuska.

6. Ki kasance mai shafa mai domin fatar fuskarki ta kasance cikin danshi, kasancewar wadansu kurajen fuskar sun fi 6ata fuska idan fuska tana bushe.


7. Yi amfani da man ‘Tea Tree’ domin ba wai kawai yana baje kurajen fuska ba ne, a’a yana rage ƙarfinsu da kuma kalarsu. Zaki sami ire-iren wadannan man shagunan sayar da kayan kwalliya na zamani.

8. Ki kasance mai yin taka tsan-tsan wajen amfani da ire-iren man shafawar da kike amfani da su a gashin kanki, ma’ana kada ki sake ya rinƙa taba fuskarki hakan
zai iya haifar miki da kurajen fuska, kasancewar waɗansu sinadaran an yi su don su taimaka wa gashin kai ne, don haka idan suka shiga ƙofofin fatar fuskarki, sai su haifar miki da matsala.


9. Ki kasance mai gasa kurajen fuskarki: 
Duk lokacin da kurajen Pimples suka fito miki sai ki samu wani ƙyalle mai tsafta, sai ki tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi, sai ki riƙa ɗora shi a kan wajen da kurajen suke, sannan ki rika gogawa a hankali, zafin ƙyallen yakan sa kurajen su motse daga nan su mutu.

10. Ki guje yin amfani da hannunki wajen fasa kurajen da suke fuskarki, domin hakan yana kara yawansu hade da sanya fuskarki ta kara cabewa.
 Allah yasa a dace

Thank you for your message.

Previous Post Next Post