MA'AURATA: SIRRIN HADA DABINO DA KWAKWA GA MA'AURATA

 SIRRIN HAƊA DABINO DA KWAKWA DA AYA GA MA'AURATA


Ana kuma samun aya a sassa daban-daban a kasashen duniya ciki har da Nijeriya.


Dabino da kwakwa da kuma aya 'ya'yan itace ne da ke da matukar farin jini tsakanin mutane musamman ma'aurata.


Galibi dai mutane kan yi amfani da dabino da kwakwa da kuma aya a matsayin wani abin kwadayi ko kuma kwalama, ba tare da sanin amfanin da suke yi a jiki ba.


Amma a shekarun baya-bayan nan labari ya sauya game da ire-iren wadannan abubuwa da a baya ake ganin cimakar marasa karfi ce ko kuma mazauna karkara, saboda dimbin binciken da masana a fadin duniya ke yi game da 'yayan itatuwa, sauyoyi da ganyaye da sauran tsirrai.


Masana da dama sun gano amfanin da suke da su ga jikin biladama, a wasu lokutan ma har da hanyoyin da mutum zai iya sarrafa su a cikin gida su kuma yi masa amfanin.


Ko wanne daga cikinsu akwai irin amfanin da yake da shi na musamman, ballanta idan aka hade su wuri guda aka sarrafa zuwa abin sha ko abinci.


DABINO


Dabino wasu 'ya'yan bishiya ne masu tsohon tarihi da kuma galibi a kasashen duniya musaman Afirka da kasashen Larabawa ake dauka a matsayin abinci.

Dabina, Aya, Kwakwa

Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA


Dabino na da danko da kuma zaki, kana yana ƙunshe da sinadaran gina jikin ɗan adama, kamar yadda Brianna Elliot, wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki ta wallafa a wata mujallar kiwon lafiya Healthline.


"Dabino na ƙunshe da sinadarai masu yaki da kwayoyin cuta ''antioxidants'' da dama, da kan taimaka wajen dakushe kaifin cututtuka masu tsananani kamar kansa da ciwon zuciya da ciwon suga da kuma cutar mantuwa," in ji Brianna.


Mutane na daukar dabino a matsayin dan iatace mai daraja da kuma tun kafin binciken kimiyya mutane da dama suka amince da shi a matsayin abin da ke warkar da wasu cututtuka musamman idan ana yawan cin sa da safe kafin a yi karin kumallo.


Haka kuma Musulman duniya kan fara cin dabino kafin su yi buda-baki lokacin azumin watan Ramadan, saboda koyi da Annabi Muhammadu (A.S).


Mutane sukan ji sun gamsu da dabino ne saboda zakiinsa da kuma sinadaran gina jikin da yake kunshe da su, kuma sukan ci danye ko kuma busasshe.


Karanta: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA


A shekarun baya bayan nan dai binciken kimiyya ya kara fito da amfanin dabino a idon duniya, inda ya samu gagarumar karbuwar da a kusan ko wane gida ba ka rasa dabino a cikin jerein 'yayan itatuwan da aka saya.


Akan kuma sarrafa shi a rika sayarwa a manyan kantunan a kasashe daban-daban na duniya.


Wata malama mai bincike kan kayayyakin abinci masu gina jiki a Najeriya, Bahijja Lawal, ta bayyana cewa idan mutum ya ci dabino guda goma da safe kafin ya yi karin kumallo, zai kara masa lafiya ta hanyar gina garkuwar jikinsa, tare da kare shi daga kamuwa da cututtuka.


"Dabino lafiyayyen dan itace ne mai albarka a jikin dan adam, don haka mai yawan cin shi ba zai yi saurin kamuwa da cututtuka ba," in ji ta.


Karanta: YADDA-AKE-AMFANI-DA-ROBAR-HANA-HAIHIWA



AMFANIN DABINO


Masana da dama a fadin duniya sun yi bincike wanda yan nuna irin sinadarai masu gina jiki da ke kunshe a cikin dabino.


Bincike ya nuna cewa dabino ya kunshi sinadaran protein da calcium, da minerals da fat, da lime, da phosphorous, da chlorine, manganese, da sauransu, wadanda duka suna da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen lafiyar jikin dan adam.


A bayanan da ta wallafa a mujallar kiwon lafiya ta Healthline, Brianna Elliot ta ce dabino ya bambanta da sauran 'yayan itatuwa wajen nagarta da kuma irin abubuwan da ya kunsa, bayan da ta kimanta zakin da yake da shi kan ma'aunin da ya kai ga da zarar mutum ya ci, yakan narke cikin jini nan take sabanin sauran 'yayan itatuwa da sai sun bi matakai daban-daban na yanayin yadda jikin dan adam ke sarrafa abincin kafin ya yi masa aiki.


"Kan haka ne mutane ke amfani da dabino wajen kashe yunwa saboda yana gina jiki tare da kosarwa na tsawon lokaci - da wannan ne za mu gane cewa dabino ya kunshi manya-manyan sinadarai na abinci, wadanda za su gina jiki da jijiya, in ji ta.


Masana kimiyya na cewa dabino na amfanar da kananan yara da matasa da 'yan wasa da ma'aikata, da ramammu, da kuma mata masu ciki.


Dabino yakan taimaka wa masu matsalolin ido gaba daya, kamar dai yadda yake taimakawa wajen kara gani, da kara karfin kunne, haka na kuma yakan sa wa mutum natsuwa tare da yi masa maganin saurin fushi ko yawan fada da mutane.


Karanta: KUSKUREN-DA-MUKE-ACIKIN-SOYAYYA



SIRRIN ƳAƳAN KANKANA DA ƁAWONTA GA MA'AURATA


Masana sun ce miyar kuka na ƙara wa mata ni'ima da ƙarfin mazakuta ga maza

Shi ya sa ake son mutum ya nike shi ya hada da madara ya sha da safe.


A matsayinta da kwararriya a fannin abinci mai gina jiki da kuma gyaran jiki, malama Bahijja ta bayyana cewa dabino kan tausasa jijiyoyi masu dauke da jini, ya gyara uwar hanji, sannan ya yi mata maganin radadi da rauni.


"Yana kuma taimakawa kwakwalwa sosai ba kadan ba, kamar dai yadda yakan taimakawa maza wajen ba su kuzarin shimfida," in ji Bahijja.


Kwararru da dama sun ce dabino yana taimaka wa masu azumi da kuma tsofaffi, yakan kuma taimaka wajen nike abincin da aka ci ba tare da bata lokaci ba, ya kuma sakar wa mutum mara ya rika yin fitsari sosai don fitar da cututtuka, ya tsarkake masa hanta, ya wanke masa koda, nikakkensa kuwa ya kan yi maganin tari, da majina.



AYA


Mai tallan aya


Masu sayar da aya suna taimaka wa ma'aurata wajen inganta rayuwar iyalinsu



Aya wata 'yar itace ce da ke girma a bangaren arewacin duniya inda ake samun yanayi mabambanta. Amma a zamanin yau ta samu shuhara a kasashen Turai.


Aya dai kamar yadda muka sani a kasar Hausa, ana kiranta da 'tigernut' a harshen Turanci, Yarabawa na kiranta da suna Ofio, a yayin da su kuma kabilar Igbo suke kiranta da suna imumu ko aki.


Menene Amfanin Aya

Karanta: HALAYEN-MATA-TA-GARI


Ba kamar yadda aka dauki aya a matsayin abin kwalama ba musamman ga kananan yara da har aka sarrrafa ta zuwa wani nau'in da ake kira dakuwa wanda ya fadada yanzu har kununta ake yi, a shekarun baya-bayan nan binciken kimiyya mai zurfi da ake gudanarwa kan cimaka yan una yadda aya ke da matukar muhimmmaci a rayuwar dan adama, kuma duka ya danganta da yadda aka sarrafa ta ko kuma yanayin yadda ake ci tsurarta.


Ana kuma samun aya a sassa daban-daban a kasashen duniya ciki har da Najeriya.


Aya na da dandano mai gardi kamar na kwakwa, amma sai dai ta fi kwakwa gardi kadan.


Sai dai kuma har zuwa yanzu akwai mutane da dama da ba su san amfanin shan kunun aya ba, inda wasu sun dauka abin sha ne kawai maganin yunwa ko kayan marmari, wasu kuma kayan zaki suka dauke shi.


AMFANIN AYA GA LAFIYAR JIKI


Aya kamar yadda kwararru suka bayyana, tana kunshe da muhimman sinadirai masu gina jiki, da inganta lafiyar jinin jiki da tsokar gangar jikin dan'adam, da ke yi wa jikin dan adam garkuwa daga kamuwa da kwayoyin cuta.


Kana takan magance masu maganin wasu illoli da matsalolin da ke damun maza da mata da makamantan su.


Kadan daga cikin sinadira masu gina jikin da Aya ta kunsa sun hada da: phosphorus, vitamin E, Fat, protein, dietary fibre, potassium, zinc, sodium, calcium, magnesium, copper, vitamin C, da carbohydrates.


Karin Ni'ima

Karanta: YADDA-ZAKI-ZAMA-KASAITACCIYAR-MACE



GA WASU DAGA CIKIN AMFANIN SINADARAN DA AYA TA KUNSA:


- Tana dauke da sinadaran magnesium da calcium da kuma iron.


-Tana samarwa da jiki sinadarin protein da kuma lafiyayen kitse.


-Tana kunshe da sinadarin vitamin B wanda ya ke amfanar da fata da gashi da kuma farata.


- Don samarwa da jiki sinadaran vitamin da minerals, ya na da kyau a rika cin gram 70 zuwa 50 na Aya a kullum.


-Aya tana da amfani saboda tana kara karfin garkuwar jiki sinadarin carbohydrates.


-Ta yawan amfani da ita, za ka gano cewa kusan ba ka rashin lafiya kuma za ka ji dadi sosai.


-Aya na inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita kuruciya, tana karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzari na zahiri da na boye.


-Haka kuma aya tana da amfani ga sha'anin da ya shafi ciki da hanji, tana dauke da sinadarin da ke hana cushewar ciki da kuma kumburi.


-Aya na taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral (maikon cikin jini) mara kyau a cikin jini.


Karanta: ABUBUWA-GOMA-10-DA-BA'A-JUREWA-SOYAYYA


KWAKWA


Dabino da kwakwa da aya



HANYOYI GUDA 5 DA KWAKWA KE AMFANI A JIKIN BIL'ADAMA


Kwakwa na daga cikin 'yayan itatuwa masu matukar amfani ga rayuwar bil'adama, kamar yadda masana a fannin kiwon lafiya suka bayyana.


Hakan kuwa in ji masana, ba ya rasa nasaba da irin sinadaran da Allah ya saka a cikin ta.


Kwakwa na dauke da ruwa, da kuma mai cikinta, baya ga hakan ana bare kwansonta a ci.


Kwakwa ya rabu kashi biyu, akwai kwakwar manja kana akwai kwakwa wacce ba ta dauke da manja.


Dukkanin nau'oin kwakwa dai na dauke da sinadarai da suke da matukar amfani ga rayuwar bil'adama kamar yadda masana suka bayyana.


Coconut

Karanta: AMFANIN-AUREN-BAZAWARA


AMFANIN KWAKWA


Wasu daga cikin alfanun kwakwa ga rayuwar bil'adama sun hada da:


-Tana dauke da sinadaran da ke kashe kwayoyin cuta da suka hada da bacteria, da virus da makamantansu, don haka tana kara lafiyar garkuwar jikin bil'adama.


- Masana sun bayyana cewa ruwan kwakwa kara lafiya da kuzari jikin bil'adama.


- Kwakwa na dauke da sinadaran vitamins wadanda ke taimaka wa sassan jikin bil'adama wajen saurin narkar da abinci.


- Tana taimaka wa masu dauke da cutar suga (diabetes), kana tana samar da garkuwa ga wadanda basa dauke da cutar.


- Tana rage barazanar kamuwa cutar kansa (cancer) a jikin bil'adama in ji masana.


Yadda ake sarrafa kunun dabino da kwakwa da kuma aya


Bayan da binciken masana ya yi nisa game da amfanin 'yayan itatuwa, da ganyaye da sauran tsirrai a fadin duniya, yanzu haka akwai hanyoyi da dama da ake hadawa da kuma sarrafa su ta yadda za su amfani a jikin dan adam a fadin duniya.


Yanzu haka akan hada kwakwa da Aya da kuma dabino a sarrafa su ta hanyar markade, wanda a yankin arewacin Najeriya ake kira kunu.


Yayin da wasu su kan sarrafa su kuma rika shan wannan hadi na kunu a matsayin nishadi ko a lokutan bukukuwa, wasu kuwa suna yin sa da gaskiyar niyyar cewa akwai amfanin da zai musu a jiki.


Ga kuma bayani kan ɗaya daga cikin hanyoyin da ake sarrafa su:


Kayan haɗi


-Dabino (daidai gwarwado)


-Kwakwa ( guda biyu ko ɗaya)


- Aya (daidai gwargwado)


- Kayan kamshi (don karin armashi)


- Sukari (idan ana bukata)


- Madara (idan ana bukata)


Matakan sarrafawa


- A wanke Dabinon sosai


- A fasa kwakwa a tsiyaye ruwan a shanye ko a sha da madarar ruwa.


- Za a hada a markade Kwakwar da dabino da Aya a tace da rariya.


- Za kuma a iya zuba madarar ruwa a sha, ko kuma haka nan.


Karanta: YADDA-AKE-RAGE-SHAAWA


AMFANIN HADINSU DUKA (KUNUN AYA) A JIKIN DAN ADAM.


Duk da cewa har yanzu akwai mutane da dama da ba su gane muhimmancin amfanin shan kunun aya ba, inda wasu kan dauka abin sha ne kawai ko kuma maganin yunwa ko kayan marmari, yayin da wasu kuma kayan zaki suka dauke shi.


Galibi dai kunun ayar akan hada ne da kwakwa da dabino don inganta dandano da kuma amfaninsa.


Shi ya sa daukacin hadin ake kiransa da kunun aya, suk da cewa ba aya zalla kadai ya kunsa ba.


Yawanci an fi sarrafawa a kasar Hausa, inda akan yi amfani da shi wajen tarbar baki, ko lokacin bukukuwa


Sai dai kuma yanzu haka a bisa kara zurfin binciken kimiyya da masana suka yi yana nuna cewa wannan hadi na dabino da kwakwa da kuma aya, ya wuce yadda aka dauke shi, saboda dimbin amfanin da suke da shi musamman idan aka sarrafa.


Baya da lafiyar jiki dan adam, masana sun yi ittifakin cewa kunun ayar yana da matukar muhimmanci ga ma'aurata musamman mata.


Masana harkokin zamantakewa da malaman addinai musamman na Musulunci za ka ji suna yawan fadakarwa game da muhimancin shan 'yayan itatuwa ciki har da su Aya, da Dabino da kuma Kwakwa wajen kara ni'imar mace da kuma kara kuzari a bangaren maza.


Yanzu haka kuma akwai kasidu da mujallu na kiwon lafiya a kasashe daban daban da ke bayyana muhimmancin aya da dabino da kuma kwakwa a jikin dan adam, musamman ma'auratan.


Kan haka ne ya sa za ka ga irin nau'ukan wadannan cimaka ke da matukar tasiri da kuma karbuwa a tsakanin al'umma musamman a kasashen Afirka.


Galibi yanzu ba ka rasa ire-iren wadannan cimaka a cikin gidajen mutane a koda yaushe, saboda wayewa game da amfanin da suka da shi a jikin dan adama.


Za kuma ka ga ana sayar da su a kasuwanni fiye da yadda aka saba gani a shekarun baya.


Hakan kuma ba ya rasa nasaba da rashin sanin amfaninsu a baya, da kuma tunanin cewa irin wannan cimaka ta masu karamin karfi ce ko kuma mazauna karkara wadanda kan su bai waye ba.



Thank you for your message.

Previous Post Next Post