AMFANIN NONON AKUYA GUDA 8 A JIKIN MUTUM

 AMFANIN NONON AKUYA GUDA 8 A JIKIN BIL ADAMA


Writer: Muhammad Abba Gana

AMFANIN NONON AKUYA GUDA 8 A JIKIN BIL ADAMA

Premium Times ta rawaito cewa hukumar bada shawara akan bunkasa ayyukkan noma na Najeriya NIFAAS ta yi kira ga mutane da su yawaita shan nonon akuya saboda kara lafiyar jiki da yake yi.

Hukumar ta bayyana cewa Nonon Akuya yafi na saniya amfani a jiki.

Amfanin 8 da nonon akuya ke yi a jikin dan Adam sune:

1. Nonon akuya na ɗauke da sinadarin ‘Protein’ da yafi na nonon Saniya. Yana taimaka wa jiki girma yadda ya kamata musammam ga yara masu tasowa.

2. Yana ɗauke da sinadarin ‘Amino Acids’ da ke ƙara garkuwan jikin mutum.

Karanta: ABUBUWA-GOMA-10-DA-BAA-JUREWA-SOYAYYA

3. Yana ɗauke da ‘Vitamin A’ da ke ƙara Ƙarfin ido.

4. Yana ɗauke da ‘Potassium’ da ke kare mutum daga kamuwa da cutar shanyewar gefen jiki, ƙara Ƙarfin ƙashi, kare mutum daga kamuwa da cutar hawan jini da makamantan su.

Amfanin Nonon Akuya

Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA

5. Yana ɗauke da ‘Phosphorous’ wanda ke taimakawa wajen fitar da ababen da jiki ba ya bukata kamar zufa, fitsari da bayan gida.

6. Nonon akuya na da saurin nika abinci a cikin mutum.

7. Yana Ɗauke da ‘Magnesium’ da ke taimakawa mutane dake fama da rashin barci.

8. Yana ɗauke da sinadarin ‘Manganese’ da ke ƙara Ƙarfin ƙashi.

Thank you for your message.

Previous Post Next Post