YADDA AKE GANE BUDURWA ME KWAƊAYI

 YADDA ZAKA GANE BUDURWA ME SON ABUN DUNIYACE SOSAI (kwadayi)Zama da matan da suke da kwaɗayi Babban barazana ce ga Soyayya, domin tana daƙushe shauƙin dake cikin Soyayya acikin ƙanƙanin lokaci. Wannan dalilin yasa mukai duba akan wasu hanyoyin da ake gane matan dake da kwaɗayi sosai. Anan ƙasa mun kawo musu kaɗan daga ciki:

1. HADA PLAN DA ƘAWAYENTA: Misali zakaga tana yawan hada baki da ƙawayenta, sai kuna hira kawai kaga wata ƙawar ta da guntun kyalle, tazo ta wuce sai itakuma budurwar taka tace wance ba maga, sannan itakuma ta waiwayo tace au wlh bangankuba sannan Azo agaida ka, sai kaji ance kekuma ya kike yawo da kyallen atamfa, sai kaji munafukar tace la ke bata bakiba ai kuwa naga kyalle agun wance tace nakine kice bata bakiba Ankwan ƙawarkine wlh kinga wane zan kaiwa yabawa kabiru (wato saurayin ta) wai zai sayo min ke natafi karna dameku ALGUNGUMA
Dolene kaikuma saurayi gabanka yafadi to suna da plan kala kala na wankar samari kodama ba ankon ba.

Budurwa me kwadayi

2. Yawan ɗaukar abu agaban saurayi tace yabiya mata

3. Yawan sauraron samari koda bama saurayin taba ita tunaninta yawan samarinta yawan hanyoyin shugowar kudinta kowa zata kula musamman ma me ungo

4. Yawan tambayarka kayi mata wani abu wanda a zahiri bai zama dole kayimata ba.


5. Nuna sha awar duk abunda tagani a gabanka kamar kuna hira taga me sarqa da ɗankunne daga nesa UWA MAIYA ZAKAJI TANA KAI KAI KAI WAIYO ALLAH JIWATA SARQA, INKUWA BABBAR MACECE CEWA ZATAI KASH INAMA KUSA ATM MUKE DASAURAN ALAYE.
kaikuma dolekasaya idan zakarane kai meneman suna.


6. Yawan baka labarin wani abu data gano a Makaranta, gidan biki ko wanigun kai jiya naga wata sarqa yaryayi wlh dana gwada kamar bani ba baka ganniba kamar yar indiya. Ko tace taga wata blackberry me saurin chating, haka dai zatai tabaka labari dan kasayamata.


7. Kokaji tana kushe saurayin wata ai jiya suka bata, ai dama dole subata kullun babarta sai tace yana bata kudin zance boyewa take itakuma tace ai marowacine duk kai akewa hanunka me sanda, da shauran hanyoyi da dama.

(RUFEWA)
KUGANE YAN SAMARI BA WAI KA KASHEWA BUDURWAR KA KUƊI LEFINE BA A'A ILLAR ACE ITA ME KWAƊAYI CE IN KA AuRETA KA SHIGA 9.
Amma kyautatawa masoyiya dayimata hidima abune me kyau da qara danqon soyayya musamman ma ace akwai alqawarin aure a tsakanin ku.

Thank you for your message.

Previous Post Next Post