YADDA AKE DAINA ISTIMNA'I

  Hanyoyin Rabuwa da Istimna'i (Masturbation)


Hanyoyin Rabuwa da Istimna'i: Haƙiƙa matsalar Istimna'i (wato Masturbation) da hausa kuma Zinar Hannu (kokuma duk wata hanya ta fitar da maniyyi bata jima'i ba, kuma ba a mafarki ba) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KAKA-GIDA Kuma tana da wahalar fita gaba ɗayanta dole sai dai albarkacin addu'a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah a zuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawaba.

An tattauna da mutane sama da dari biyu (200) a wannan satin yawanci suna kukan yaya zasu yi su rabu da wannan matsalar sudaina yi, suna cewa koda sun daina suna kara komawa basa'iya bari, Wasu daga cikinsu suna cewa gaba daya basa iya haddace karatu adalilin matsalar aikata Istimna'i ta kawo musu.

Karanta: AMFANIN-AUREN-BAZAWARA

Wasu Kuma suna cewa haka kawai suke zubar da maziyyi koda wa'azi sukaji anayi akan mace, wasu kuma na cewa kankantar gaba ne yake damunsu, Wasu Kuma Ya haifar musu damatsalar ido, Wasu Kuma tsananin ciwon baya, Dan Allah ai Ya kamata kodan wannan mutumya tuba yabar aikata wannan abin.

Mafiya yawan samari suna yine bisa niyyar wai zasu Kaucewa zina. Basu san cewa shima wannan babban kaba'ira bane.

Karanta: ABUNDA AKE NUFI DA CUTAR SANYIN GABA DA HANYOYIN MAGANCE SU

Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala'in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.

Kuma kamar yadda zina take da mutuƙar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalin sa, da gurbata tunanin sa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa.


Yadda ake daina Masturbation

Karanta: YADDA-AKE-RAGE-SHAAWA


To hakanan shima Istimna'i yake lalata rayuwar mutum da mutuncin sa da lafiyarsa. Lallai wajibine ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya,yanisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna'i, da sauransu. Kamar yadda ake ta faÉ—a anan a kafafen Wa'azantarwa da faÉ—akarwa. Babbar hanyar da zaka bi/zaki bidomin rabuwa da wannan bala'in sun haÉ—a da:

1. Yin aure

2. Yawaita azumi

3. Nisantar duk wani hoto ko video mai nuna tsaraici. (Ka gogeshi daga wayarka)

4. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.

5. Dena abota da fitsararrun abokai Qawaye.

6. Nisantar duk wajen da ake chuÉ—anya tsakanin maza da mata.

Karanta: YADDA-AKE-SADUWA-DA-AMARYA-DAREN-FARKO

7. Ka daina zama kai kaÉ—ai a cikin É—aki in dai ba ibada kake yi ba.

8. Yawaita karatun Alqur'ani da zikirin Allah da sauran ayyukan alkhairi.

9. Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da ƙoƙarin koyi dasu.

10. Tuna Allah ako yaushe da kuma tuno kusancinsa gareka aduk inda kake.

11. Tuna kusancin ajalinka, fitar ranka, kwanciyar ƙabarinka, hisabinka, da kuma masauƙin ka na ƙarshe. Wuta ko Aljannah.

12. Fita daga duk wani Group ko shafi na batsaa Facebook ko Whatsapp wanda suke Æ™unshe da abubuwan batsa, tare danisantar Friends masu sharing din abubuwa irin wannan. 

Thank you for your message.

Previous Post Next Post