BAYANI AKAN GASKIYAR FATALWA

 SHIN DA GASKE AKWAI FATALWA?

Me ya sa ake ganin fatalwa, kuma me masu ganinta suke gani?

Reference: BBCHAUSA

Jin muryoyi masu ban tsoro da tsakar dare. Gane-ganen abubuwa barkatai. Lamarin da ke kada hantar mutum.

Mutane da dama sun fuskanci yanayi mai firgitarwa wanda ba za su iya yin bayani ba.

Misali, mazauna wani gidan gona a wata gona da ake kira 'Pennyford Farm'.

Waɗanda suka taɓa zama a gidan, wanda ke Wales ta arewa da ke Birtaniya, sun yi iƙirarin cewa akwai mutanen ɓoye a gidan lokacin da suke zaune a gidan a shekarun 1990.

A hirarrakin da mai gidan ya yi da kafofin yaɗa labarai, ya yi iƙirarin cewa wasu abubuwa ne suka riƙa bayyana jikin bangon gidansa da ke Wales.

Kuma daga cikin iyalansa, babu wanda ya iya gane abubuwan da ke bayyanan.

Bayan haka ne wasu abubuwa da ba a saba gani ba suka soma faruwa a gidan nasa.

Fatalwar wata budurwa da ta mutu da juna-biyu aka kuma binne ta a gidan gonar ce ta fara bayyana a gidan nasu.


What is ghost

Karanta: ABUBUWA-GOMA-10-DA-MAZA-KE-SO


Wani shirin BBC mai taken "The Girl, The Ghost and the Gravestone" ya yi bincike game da jita-jita da tatsuniyoyi da almarar da ake yaÉ—awa game da fatalwa.

Shirin ya yi nazari a kan gidan gonar tare da tattaunawa da waÉ—anda suka fara zaman a gidan.

Shirye-shiryen 'BBC Three' da 'BBC Wales' duka sun yi magana kan gidan gonar.

Mai gabatar da shirye-shirye a 'BBC Radio One', DJ Sian Ellery ya yi ƙoƙarin fito da sahihan bayanai game da abin da ya faru a gidan.

Sian Ellery shi ne mutum na baya-bayan nan da ya yi yunƙurin fito da binciken kimiyya game da fatalwa.

Karanta: DIFFERENCE-BETWEEN-MISCARRIAGE-AND-ABORTIONS

BBC Three ta tattauna da wasu masana kimiyya guda biyu.

Masanan sun yi bayani kan dalilan tunani da na muhallai da ke sanya mutane yin imani da ganin fatalwa.

Duk da rashin gamsasshiyar hujja a kimiyyance, mutane sun daÉ—e da yin imanin cewa akwai fatalwa kuma tana bayyana.

Dakta Chris French shugaban cibiyar binciken tunanin ɗan'adam na jami'ar Goldsmiths da ke London, ya ce duka labaran fatalwa da ake gani na da alaƙa da lalurar dannau.

A lokacin da mutane suka fara bacci amma idanunsu a buɗe (baccin zomo), ƙwaƙwalwarsu kan tsayar da gangar jikinsu daga motsi.

A wannan mataki sukan ji kamar ba bacci suke yi ba, amma kuma ba sa iya motsi.

Sauran alamomin lalurar dannau, sun haɗa da jin kamar wani mutum na cikin ɗakin da kake, yana danna ka, kamar yadda bayanai daga shafin intanet na hukumar lafiyar ƙasar suka nuna.

Baccin-zomo, wani yanayin bacci ne da ake alaƙantawa da mafarki. Haka kuma yana haifar da jiye-jiye da gane-gane yayin da mutum ke cikin barci.

Karanta: YADDA-ZA-KAYI-IDAN-MACE-BATA-KARBI-SOYAYYAR-KA-BA

Ya ce "dannau wani nau'i ne daga cikin matsalolin bacci. Abu ne da ke gigita mutane.

"Daya daga cikin dalibai na ya gaya min cewa yakan tashi barci a firgice inda yake ganin baƙar kyanwa a karƙashin gadonsa".

'Yakan ga kyanwar a dungure yayin da bakin yawu na fita daga bakinta."

"Don haka, tun da lalurar dannau, wani abu ne da kowa ya sani, haka kuma ana yawan samun ƙaruwar mutanen da ke iƙirarin ganin fatalwa a lokacin da suke barci, kamar yadda Chris ya bayyana, ya na mai cewa matsalar na haifar da ganin wasu abubuwa.

Karanta: YADDA-AKE-KIYAYE-LAFIYAR-IDANU

Dakta Shane Rogers Farfesa ce a fannin gine-gine da muhalli a jami'ar Clarkson da ke New York.

Suna gudanar da bincike kan alaƙar da ke tsakanin gidajen da ake samun fatalwa da hunhuna.

Dakta Shane ta fahimci cewa É—abi'ar ‘ya’yanta ta sauya bayan da suka ga hunhuna a wasu tsoffin gidaje.

Ta kuma kalli wasu fina-finai kan gidajen da fatalwa ke bayyana kuma da yawa daga cikinsu na da alamun hunhuna.

An kuma bayar da rahoton É—abi'un da mutane ke nunawa bayan ganin hunhunar.


ALAƘA TSAKANIN HUNHUNA DA FATALWA

A cewar Hukumar Kiwon Lafiya ta Kasa, hunhunar da ake samu a cikin danshi, da daskararrun gine-gine na iya haifar da matsalolin numfashi da kuma matsalolin gani.

Sakamakon abubuwan da suke gani cikin barci na haifar musu da tsoro ko razani a cikin barcin.

Dakta Shan tare da tawagarsa sun karbi bayanai kan hunhuna daga wurare 27 da ake kallo a matsayin wuraren fatalwa.

Tawagar masu binciken ta gano babbar alaƙa tsakanin funfuna da gidajen fatalwa.

Dakta Shan ya ce daga binciken da muka yin mun gano cewa akwai alaƙa mai karfi tsakanin hunhuna da gidajen fatalwa.

Karanta: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAÆŠUWA


IMANI DA FATALWA

Dakta Chris French wanda ya halarci shirin a matsayin masani, ya ce akwai bayanai uku da masu iƙirarin cewa suna ganin fatalwa ke yi.

Ciki har da imani da fatalwar, "idan ka yi imani da ita, to hakan kan sa mutum ya yi ta ganin fatalwa cikin barcinsa".

Dakta Chris ya ce "idan mutane suka ji kalmar fatalwa, sukan riga ganinta tana tafiya a jikin bango".

Mutane kan bayar da irin waÉ—annan bayanai, to amma ba su da yawa, labari ne na jita-jita.

Mutumin da baya iya barci na tsawon lokaci, ko yake cikin damuwa ko yake da da zafin jiki za su iya samun matsalar raya faruwar abubuwa a ransa.

Dakta Chris ya ce idan aka nuna maka tsoffin gine-gine aka kuma shaida maka cewa gidajen fatalwa ne za ka iya raya ganin fatalwa a cikin barcinka.

"Hakan ba zai faru ba idan ba a gaya maka haka ba''.

Karanta: YADDA AKE RARRASHIN BUDURWA


ALAƘAR FATALWA DA KIMIYYA

Akwai kuma wasu bayanai guda biyu na kimiyya game da fatalwa.

Daya daga cikin bayanin na cewa: Akwai wani karfin maganadisu wanda ke sauya bayanan da kwakwalwa take sarrafawa, lamarin da kan iya haifar da tunanin ko ganin wani abu da babu shi.

Wasu kuma na alakanta lamarin da wasu sautuka masu kama da na rauhanai wadanda ke da wahalar fahimta ga dan’adam.

Wannan bayani na cewa akwai wani irin sauti da kan shafi kwayar idin dan’adam, ya sa ta ta kada.

Wannan na haifar da gane-gane.

Domin nazarin wadannan bayanai biyu, Dr. Chris da tawagarsa sun kirkiri wani daki mai ban tsoro.

Karanta: YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA


ABIN DA BINCIKE YA NUNA

A lokacin binciken an saki wasu sautuka da ke kasa da yadda kunnen dan’adam zai iya fahimtarsu da kuma wani karfi ma maganadisu.

Dr. Chris ya ce “Mutanen sun bayyana cewa sun tsinci kansu a wani yanayi da ba su saba da shi ba a cikin dakin, sannan mutum takwas daga cikinsu sun ce sun shiga hali na firgici.

“Matsalar dai ita ce, a lokacin da muka yi nazari kan sakamakon, babu wani banbanci a kan lokacin da aka kunna sautin ko maganadisun da kuma lokacin da ba a kunna ba.”

Ya kara da cewa “Idan ka ce wa mutane za ku shiga wani yanayi na daban idan kuka shiga wancan dakin, wasu mutanen za su yi tsammanin hakan za ta faru, to amma wannan ba wani abu ba ne face tasiri abin da ka fada.”


Thank you for your message.

Previous Post Next Post