AMFANIN SANIN ABOKIN SAURAYI

AMFANIN SANIN ABOKIN SAURAYIN KI.


Zuwa ga Mata Mutanen Mu!!!

Wanene Abokin Saurayi???
Abokin Saurayi Shine Wanda koda yaushe ko a cikin yawancin lokuta suna tare dashi. 
Wanda suke yawan mu'amala ta yau da kullum.

Wanda yasan komai agame da saurayin ki. Wanda zai iya wakiltar saurayi ki aciki. Wasu abubuwa na rayuwa.

Kada Kiyi Kuskuren Rashin sanin Ɗaya daga cikin abokan saurayin da kike Soyayya Dashi.

Idan kina Soyayya da wani saurayi koma wanene shi, ko ta wace siga yazo miki, to ki tabbatar Kinsan waye abokin shi ɗaya ko biyu.

Abokin Saurayi
Amfanin Sanin Abokin Saurayi.

Yana daga cikin amfanin Sanin Abokin Saurayin ki Shine Kisan waye Shi Saurayin naki.

Duk wani Mutumin Kirki to abokan shi mutanen kirki ne, Haka Duk wani Mutumin banza abokanshi mutanen banza ne.


Bazaka taba ganin Mutumin Kirki yayi abota da na banza ba, Yin hakan zai zubar mishi da ƙima, sannan Za'a na zargin shima bana kirki bane.

Irin Halayyar da kika ga abokin saurayin ki To Shine Halayyar Saurayin ki. 

Domin Koshi Na Kirki ne idan yayi abota da mutanen banza zasu iya rinjayarshi zuwa ga abunda Ba'a so. Amma idan yayi hakan da wata manufa wannan kuma an shiga wani babi na daban.
Idan akwai me wata shawarin shima ya ajiyeta wajen Comment.

Allah Ya Bamu Abokan Kirki, Allah Yasa Muma Mu Zama Na Kirki. Kuma Mata Allah Ya Baku Samarin kirki.

 ABUBUWAN DA KESA MU GUJEWA MATA

Akwai wasu abubuwa dake sanya maza guduwa daga wurin ƴan matan su. Batare da anyi aune ba sai kaga mace ta rasa saurayin ta.


Halaye ne irin na matan Wanda kuma munyi munyi su gyara su kunƙi gyarawa daga nan sai mu fece.


Karanta: ABUBUWA GOMA 10 DAKE CUTAR DA MUTUM KULLUM


Ki Sani:
- Mu maza muna son mace ne ba dan Kyawunta ba kawai.
- Mu maza muna son mace ne ba dan Muyi Soyayya ba kawai.
- Mu maza muna son mace ne ba dan S*x ba kawai.
- Mu maza muna son mace ne ba dan itace kalar sakawa a gaban mota ba kawai.


karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-NUNAWA-MACE-SOYAYYA


Sai don Muna son *Wife Material* Wato:
* Macen da take da addini.
* Macen da take da Ilimin Zama da mutane
* Macen da ta iya kula da namiji.
* Macen da zaka bata ashirin ta baka Hamsin.Ku Shiga Nan 👇🏻


* Macen da zaka bata Magi ta Baka Miya.
* Macen da Zaka nemi shawari ta baka Cikin Hikima.
* Mace Mai hankali da tsoron Allah.

Kaɗan daga ciki kenan amma sun nika haka yawa.

Waɗannan sune abubuwan da muke so a wurin mata, duk namijin da bai samu irin su ba to zaki ga yana ƙoƙarin guje miki.

Menene Mafita Shine Ki Gyara, Duk abunda kike aikatawa Ki Tabbatar ba mai ce miki babu Kyau. Kiyi abunda ƙuda Zai biki.

Karanta: AMFANIN GAUTA A JIKIN MUTUM GUDA GOMA

 

Mace mai kyan hali fa Bata yin kwantai, Wawiyar macen da bata san menene duniya ba ce ke barin maza su guje mata.

Kina mace idan namiji ya yaudareki wallahi kece kika jawo.

(Tini na Shaƙewa ɗan Banza Maƙogoro da Kalaman Soyayya.)

Ƴan Mata Ku Gyara Mu Tafi Tare.

Idan Akwai me wata shawarar ina Jiran Comment Naku.


Allah Ya Bamu Ikon Gyarawa. Ameen

Thank you for your message.

Previous Post Next Post