AMFANIN SANIN ABOKIN SAURAYIN KI.
Kada Ku Manta Kuyi Download na Application Namu domin kuna samun Sabbin Posting Namu Akan Lokaci👇🏻
Zuwa ga Mata Mutanen Mu!!!
Wanene Abokin Saurayi???
Abokin Saurayi Shine Wanda koda yaushe ko a cikin yawancin lokuta suna tare dashi.
Wanda suke yawan mu'amala ta yau da kullum.
Wanda yasan komai agame da saurayin ki. Wanda zai iya wakiltar saurayi ki aciki. Wasu abubuwa na rayuwa.
Kada Kiyi Kuskuren Rashin sanin Ɗaya daga cikin abokan saurayin da kike Soyayya Dashi.
Idan kina Soyayya da wani saurayi koma wanene shi, ko ta wace siga yazo miki, to ki tabbatar Kinsan waye abokin shi ɗaya ko biyu.
Amfanin Sanin Abokin Saurayi.
Yana daga cikin amfanin Sanin Abokin Saurayin ki Shine Kisan waye Shi Saurayin naki.
Duk wani Mutumin Kirki to abokan shi mutanen kirki ne, Haka Duk wani Mutumin banza abokanshi mutanen banza ne.
Bazaka taba ganin Mutumin Kirki yayi abota da na banza ba, Yin hakan zai zubar mishi da ƙima, sannan Za'a na zargin shima bana kirki bane.
Irin Halayyar da kika ga abokin saurayin ki To Shine Halayyar Saurayin ki.
Domin Koshi Na Kirki ne idan yayi abota da mutanen banza zasu iya rinjayarshi zuwa ga abunda Ba'a so. Amma idan yayi hakan da wata manufa wannan kuma an shiga wani babi na daban.
Karanta: KUSKUREN-DA-MUKE-ACIKIN-SOYAYYA
Idan akwai me wata shawarin shima ya ajiyeta wajen Comment.
Allah Ya Bamu Abokan Kirki, Allah Yasa Muma Mu Zama Na Kirki. Kuma Mata Allah Ya Baku Samarin kirki.