HANYOYI GOMA 10 DA AKE SACE ZUCIYAR MACE

HANYOYI GOMA 10 DA AKE SACE ZUCIYAR MACE

Hanyoyin Da ake sace zuciyar mace nada dama sosai amma zamu tattauna kaɗan daga cikin su a taƙai ce. Zan kawo muku Hanyoyi Guda 10 da ko wace mace ke so ayi mata su amma bazasu faɗa cewa suna so ba, amma idan kayi mata zata ji daɗi sosai kuma zata Rikice akan ka.

1. Yawanta Kiranta da Safe.

Kiran mace da safe nada Matuƙar amfani kuma yana da rasiri sosai a Soyayya. Ka kira budurwar ka da safe ka Tambaye ta Yakike, ka maga kalamai masu daɗi. Daga ƙarshe kayi mata Addu'a.

2. Kar Kayiwa Mace Ƙarya.

Ƙarya a Soyayya Babbar Barazana ce dake ruguza Soyayya komai Ƙarfin ta komai Jimawar ta. Mata basa son namiji mai ƙarya wato Maƙaryaci. Duk abinda zaka faɗa mata, ka faɗa mata gaskiya. Amma kasan hannun ka😂 

Duk Macen da ta yarda dakai, Zata Fahimce ka, ba sai ka faɗa mata gaskiya ba,

Macen data Fahimce ka zata Yarda Dakai, Ba sai kayi mata ƙarya ba.

3. Kana Nunawa abokan ka cewa kana sonta akan idonta. 

Kunsan Mata da Son Zugi kuma suna son ana yabon su. Kana Yabon ta da kalamai masu daɗi a gaban abokan ka hakan nasa mata Shauƙi da ƙara sonka.


Karanta: YADDA-AKE-SA-BUDURWA-TA-KWAREWA-SOYAYYA

4. Ka Zama Mai Iya Controlling ɗin Matsalolinta. 

Ka zama mai tsaya mata a komai na rayuwar ta, karka danne mata hakki. Ka share mata kuka lokacin da take buƙata. Ka zama kusa da ita aduk lokacin da take cikin yanayin Ƙunci.


5. Kana Yawan mata Kyauta.

Kunsan Mata Da Son Kyaututtuka kuwa? Idan bakayi ma ka shirya yiwa Budurwar ka Kyauta mai kyau, ka zabi Abubuwan da tafi so kana Bata su a matsayin Kyauta.

6. Ka zama Mai Ban dariya a wurin ta.

Mata suna son namijin da ya iya ban dariya. Wanda idan sun zauna dashi koda yaushe zai iya yaye musu kaɗaici, yakuma saka su Murmushi da dariya don ɗebe kewa. Ƙwarewar ka a wannan fanni zaisa mata suna sonka sosai.

7. Inda Hali Kuna Fita Yawon Buɗe ido.

Mata sun kasance yawanci suna Gida ne a zaune Kullum sai aiki  gida ko Makaranta. Da zarar mace ta samu namijin da zaina kaita wuraren buɗe ido to zataji Kamar Ta zama Ƴantacciya ce don haka Kaine zatana ɗauka a matsayin wanda ya ƴantata.

Yadda ake sace zuciyar mace

Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA

8. Wani Lokacin Kana Zuwa da Abokanka Wurin Ta Kuyi Hira Tare.

 9. Ka Nuna Mata Baka da Kowa sai Ita, Kuma Kayi Mata Alƙawari Kuma Ka Riƙe sosai, itakuma Zata Yarda Dakai.

10. Karka Wuce Gona da Irin Idan Kuna Hira koda kuwa cikin Wasa ne. A kiyaye

11. Ka Nuna Mata Idan Tana Tare dakai Tana Cikin Tsaro Da Rashin Fargaba, ko ƙunci ko damuwa duk ka yaye mata su. Kuma Komai Zaka Iya Yi Dan Ita.

12. Kada Ka Karya Mata Zuciya.

You read:


Thank you for your message.

Previous Post Next Post