Abu Biyar Da Zaka Sani Akan Sabon Mai Kuɗin Duniya Arnault Da Ya Sauke Elon Musk

 Abu Biyar Game Da Sabon Mai Kuɗin Duniya Arnault Da Ya Sauke Elon Musk


Bernard Arnault ya tara dukiyarsa daga kamfanin LVMH da ya mallaka


Bernard Arnault


A makon da ya gabata ne Elon Musk ya sauka daga matsayi na ɗaya a jerin masu arziki na duniya baki ɗaya bayan raguwar darajar hannun jari a kamfaninsa na Tesla.


A cewar mujallun Forbes da Bloomberg, Bernard Arnault ne ya sauke Mista Musk daga matsayin, wanda shi ne shugaban kamfanin ƙera kayan ƙasaita na LVMH.


Mista Musk ne ke da mafi girman hannun jari a kamfanin ƙera motoci masu aiki da lantarki na Tesla, inda yake da kashi 14 cikin 100.


Karanta: YADDA ANGO ZAI GYARA KANSHI KAFIN AURE


A cewar Forbes, dukiyar Mista Musk yanzu tana wajen dala biliyan 178. Shi kuwa Bernard Arnault na da biliyan 188.


Mista Arnault na kula da hamshaƙin kamfanin LVMH da ke samar da kayayyakin ƙwa da tufafi 70, cikinsu har da Louis Vuitton da kuma Sephora.


Ɗan Faransa ne

An haifi Bernard Arnault a shekarar 1949 a ƙasar Faransa.


Mazaunin birnin Paris ne, wanda ya tara akasarin dukiyarsa ta hanyar kamfaninsa na LVMH.


Shi ne Bature na farko da ya taɓa zama attajiri mafi arziki a duniya.


Yana da 'ya'ya biyar kuma huɗu daga ciki suna aiki a LVMH.


Karanta: YADDA AKE RAGE SHA'AWA


Ba ya amfani da shafukan sada zumunta

Da zarar mutum ya duba sunan Mista Arnault a dandalin sada zumunta zai ga shafuka masu yawa ɗauke da sunansa, amma kusan dukkansu na boge ne.


Rayuwarsa ta sha bamban da ta tsohon mai kuɗi Elon Musk wajen nuna kai da kuma fantamawa.


Hasali ma, Bernard Arnault ya ce ya sayar da jirginsa da ya mallaka saboda ana yawan tsokanarsa a Twitter cewa yana yawan amfani da shi.

Ya farauto zuciyar matarsa da kiɗa


Who is Bernard Arnault

Bernard Arnault da matarsa Helen 


Bayanan hoto,

Bernard Arnault da matarsa Helen a watan Yuni yayin wani biki a birnin Paris


Arnault sananne ne wajen kaɗa garayar turawa da ake piano.


Wannan dalilin ne ya sa matarsa Helene Mercier ta ƙyasa saboda irin yadda yake buga kiɗan Copin da sauran salon kiɗa na zamanin baya a piano.


Kazalika, ɗan yawon neman zane-zane ne wanda ake kira art collector a turance.


Karanta: YADDA AKE TSARA MACE FARKON HAƊUWA


Yana zaga kanti 25 a rana ɗaya

Attajirin mai shekara 73 kan za ga kantinansa da na abokan gogayyar kasuwanci duk ranar Asabar.


Rahotanni sun ce dattijon kan je kanti 25 jimilla a duk irin wannan rana.


Mai taimako ne

Kazalika, tsohon ya daɗe yana ba da kuɗaɗe wajen gudanar da ayyukan al'umma a faɗin duniya.


An ruwaito cewa Bernard Arnault ya ba da kuɗi dala miliyan 212 don sake gina gagarumin ginin coci na Notre-Dame Cathedral da ke birnin Paris na Faransa bayan gobarar da ta afku a Afrilun 2019.

Thank you for your message.

Previous Post Next Post