MENENE CRYPTO DA BLOCKCHAIN

MENENE CRYPTO KO BLOCKCHAIN?


Crypto: fasaha ce ta kasuwanci wadda suke bada damar hada hada ta kudi da kuma kadarori a tsakanin miliyoyin mutane ba tare da sun san junansu ko sun taba ganin junansu ba.

TA YAYA ZAKA ZAMA ÆŠAN CRYPTO
Akwai hanyoyi da yawa da ake cin moriyar crypto misali:
1. wadanda ba sai ka saka kudi ba: bawai lallai sai kana da jari zaka iya cin moriyar crypto ba, a'a ire iren wadannan hanyoyin basa bukatar ko sisin kobo kafin ka fara samun kudi a cikin crypto sai dai sukan É—auki lokaci kafin ka fara morarsu. 

Misalin wadannan hanyoyin sune kamar mining zaka iya yin mining na coin daga baya kazo ka sayar dashi kamar a kwana kwanan nan anyi mining na Pi network wanda kullum sau daya zaka shiga application din amma a kasa da shekara daya zaka iya samun 1000pi wanda kuma a wulakance zaki iya sayar da duk guda daya 200 zuwa 250 kinga a kasa da shekara daya a mining din pi zaki samu kudin da yakai 200,000 zuwa 250,000. 

Kamar misalin sweat coin shima mining ne da suke bayar da coin dinsu a yayin da mutum yake yin tafiya, tafiyarma ba zasu barka kayi a banza ba duk takon kafa 1000 da zakayi zasu baka sweat coin guda 1,

Remitano shima mining ne, kamar satoshi, da dai sauransu wanda suna nan bila adadin.


Misali na biyu na hanyar da ba sai mutum ya saka kudi ba akwai referral zasu baka dama kana yiwa mutane register suna biyanka kwanan nan binance sun biya Naira 2,100 ga duk mutum É—aya da kayiwa register, yanzu haka akwai wallet din da take biyan 500 ga duk mutum daya da kayiwa register kuma wallahi register zaka iya yiwa mutum dari a rana kwata kwata bata da wahala kaga a rana zaka iya samun 50,000 albashin malamin makaranta na wata guda kuma duk sati suke biya. suma ire irensu suna da yawa.


Misali na uku na hanyar da zaki samu kudi ba tare da ka saka KuÉ—i ba akwai aiki da exchangers kuma aikin nan ba wani waje zaka je ba kana kwance a É—akinka zakayi kuma su biyaka kuÉ—aÉ—e masu matukar yawa dan wallahi akwai exchanger da zata biyaka sama da million daya a wata kuma aikin duk da zakayi a waya ne ba wai wani waje zasu ce maka kaje ba.



2. Hanyoyin da zaka saka KuÉ—i ka samu KuÉ—i: yar uwa kada ki tsorata dan ance za'a saka kudi komai kankantar kudinki zaki iya sakawa 2k ne 3k ne 10k ne daidai jarinki daidai ribarki kamar dai sauran kasuwanci da muka sani. 

misalan wannan hanyoyin sune akwai trading zaka sayi coin kici riba kadan ki sayar, akwai holding shikuma zaka sayi coin ka ajiye na tsawon lokaci wanda a irin haka zaki iya samun riba linki sama da 100 na kudinki, idan kina so ki tabbatar da hakan kije ki bincika nawane farashin bitcoin a 2014 da kuma yanzu zakiga a wancan lokacin ko Naira 5 baikai ba amma a yanzu da nake wannan rubutun bitcoin yana sama da million 15.

A takaice crypro ta azurta mutane dayawa kuma ta baiwa miliyoyin mazaje hanyar dogaro da kai.

Abu mafi muhimmanci a game da crypto shine ilmi, kamar yadda na fada crypro ya azurta mutane dayawa haka kuma ya talauta masu kudi dayawa, wadanda sukayi karambanin shiga ba tare da ilmi ba.



Thank you for your message.

Previous Post Next Post