ZAFAFAN WASIKUN SOYAYYA

ZAFAFAN WASIKUN SOYAYYA

Kada Ku Manta Kuyi Download na Application Namu domin kuna samun Sabbin Posting Namu Akan Lokaci👇🏻 


Waɗannan Wasu daga cikin kyawawan kalaman Soyayya kuma masu SAURIN SACE ZUCIYAR mace Muka kawo muku domin jin daɗin ku.


Acikin Kowane dare nakan kwana da farin ciki a cikin zuciyata Tare Da sanin cewa Na Mallaki mafi kyawun mace a duniya. Kuma har ma ina jin daɗi Da farin ciki idan na farka kowace safiya saboda koyaushe ina farkawa ne da tunani mafi kyawun abinda kike fada mini na Kalamai Masu Dadi, da kuma wanda zasu faru dani Dake a rayuwa - Sahibata Kin bani farin ciki mara misaltuwa kuma kwanciyar hankalina Ya Samu Ne A tare Dake, Soyayyar ki cikin zuciya ta Batada Iyaka. Ina son ki fiye da irin Son Da Nakewa kaina Muradina.
Soyayyar Ki ta sanya kyakkyawar waƙa a cikin zuciyata, wacce take sanya zuciyata cikin farin ciki kowace rana. Kin shigo rayuwata kin sanya Ta Cika Da Soyayyar ki, kuma ba tare da kin bincika ba. Lallai kin Mallaki albarka Har Tayi miki sutura kuma burina shine koyaushe Mu girmama juna, Tallafawa Juna, Tare da kare juna da soyayya har zuwa ƙarshen zamani Ma'ana Qarshen Rayuwa. Ina son ki fiye da taurarin dake Haskaka Sararin Samaniya. Sonki Tamkar hasken farin watane wanda ke Haskake Sararin farfajiyan Samaniya dake cikin Zuciya ta.


Ya Ke Mamallakiyar Zuciyata, ina son ki sani cewa zan rayu a duk tsawon rayuwata ina mika godiya ga Allah (S W A) bisa ni'imar da yayi Miki Ta Iya magana mai kyau, Kin san yadda ake kulawa da Soyayya, ko Shafin Yanar Gizo Ta Newlovevoice Bazai Nuna Miki yadda ake rubuta kaman Soyayya ba. Ina so na Tabbatar miki cewa kece ke kadai, kamar yadda ke ma a gareki ni kadai ne. Ina jin wani Farin ciki sabo Kullum don samun ki a cikin zuciyata. Kuma ina mana fatan wata kyakkyawar gobe tare da ke a rayuwata. Ina son ki fiye da yadda kike tsammani, Abar ƙaunata.

.

BabyNa, ki sani cewa na san ba sai na tuna miki yadda idanunki suke da ban sha'awa da kyau ba. Duk lokacin da na kalli idanunki zan ga yadda zamantakewar mu tare da Rayuwa Mai Dadi zata kasance Tsakanin mu a nan gaba. Ni dai ba zan iya dauke idanuna daga kanki ba; akan wannan kyakkyawar fuskar taki. Kina da kyau idan kika Sa murmushi a fuskarki yayin da idanunki kyawawa ke haskaka duniyar xuciyata ta. Ina son ki sosai, kyakkyawata. 

Dole ne in zama mutum daya mai sa'a a cikin wannan duniyar dan samun ki a rayuwata. Kin fi karfin abin da zan yi wa mace fata. Saboda kin mallaki Abubuwa da yawa fiye da yadda zan iya nema. Lallai kece aka aiko mini domin Nayi rayuwa mai inganci. Zan rayu a sauran Abunda Ya Rage na rayuwata ina mai girmama ki, girmamawa da kuma kaunarki na duk wani numfashina. Ina son ki har zuwa ranar da Rana zata Tafi Amma bazata dawo ba gimbiyata.
Assalamu'alaiki Yakike hubbyn Sona da fatan kin tashi lafiya. Ina Fata Zaki Kasance Cikin Irin Matan nan Da Suke da Rabo a Duniya, Wa'yanda Suke Karban Masoyansu Hannu Biyu. Kada Ki Taba Cewa Masoyin Bakya Son Shi, Domin Hakan Yakan Janyo Rugewar Zuciyarshi a Tare Da Burin Shi. Nayi Tafiya Mai Tsawo Dayawa dan Ganin Murmushinki, Na Manta da Matsayi na domin Nuna Qauna Agareki. Na Qanqantar da Kaina Domin ki Yarda Dani. Na Shiga Hali na Kadaici a Da, Samunki Babban Nasara Ce cikin Rayuwata. Amincewarki Nake Nema domin Rubuta Labarin Soyayyarmu Jikin Bango Mafi Girman Daraja ajikin Dutsen da Masoya Suka Kasa Isa. Bawai Iya Kalliyarki Ce Ta Jawo ni Wurin ki Ba, Ba Iya Tafiya Ba, Ba Iya Zance Ba, Ba Iya Kallo ba, Ba Kyawawan Idanu Ba, Ba Kyakkyawan Fuska Ba, Ka Kyakkyawan Surar Jiki Ba, Sai Dan Allah Nake Qaunar Ki..

Nazo Gareki Tare Da Marmarin Zaki Dubeni da Zuciya Irin Taki Fara Mai Farin Hali, Ina Miko Miki Kalma irin Ta So, Domin Dacewarki Da Ita. Duba Ga Irin Yadda Kike Gidanar Da Rayuwarki Cikin Tsari Mai Kyau, Kin Iya Magana A Nitse, Bakya Fada Da Kowa, Kin Iya Murmushi, Maganarki Mai Zaki, Kinada Kamala, Araina Nake Jin Zaki Iya Soyayya, Domin Kinada Ilimi, Hankali, Tarbiya Irin Ta Iyaye, A cikin Zuciya Har Wani Tafasa Take idan Na Kalli Tafiyarki, Jikina Bari Yake Yayi dana Ke sauraron Muryarki. Idan Na Jima Ina Kallon Ki Mantawa Nake Da Kowace Mace a Rayuwa Ta Ke Kawai Nake Kallo Da Gani. Idan Kika Amince Da Soyayya Zan Saki Cikin Wata Aljannan Irin Ta Duniya Wacce Baki Taba Shiga Ba. Da Zan Samu Soyayyar ki Da Nafi Kowa Farin Ciki Domin Kece Silar Kasancewa Ta a Cikin Wannan Hali. Inaso Na Fara Soyayya Dake, Amma Inajin Tsoro Ki Yaudareni. Inason Na Hada Inuwa Daya Dake, Kadewar Ganyen Bishiyarki Nake Tsoro. Ina Bukatar Jin Sanyi Mai Sanyaya Ruhi Irin Naki, Saidai Banason Kisa naji Zafi. Amma Ina Saka Rai Cewa Ke Ba Irin su Bace, Kina Da Tausayi Tare Da Kyakkawar Zuciya.


.

Abunda Zuciya Take So, shine Qafa Yake Bibiya, Zuciyata Ke ta Hango Qafafuna Ke Suka Biyo, Saboda Irin Tarbar da Kika Min Dakuma Irin Kulawa Da Kike bani Yake sa Naji Tamkar ni Dake Mata Da Miji Ne. Kece Rayuwata, Kece Farin cikina, Kece Silar Dariyata, Idan Nayi Fishi Kece Mai Sani Murmushi, Idan Nayi Kuka Kece Me Sani Dariya. Amanar Zuciyata Yana Hanunki Idan Kika so Ki Rikeshi, Idan Kika so Ki Jefar, Amma Ki Sani Idan Babu Ke, Ni Bazan Yi Rayuwa Ba. Idan Kika Jefar Da Soyayyar da nake miki, To Kamar Kina Kunna Wutar yaki ne a cikin Qoqon Zuciyata, Farin ciki Zai Qaurace, Zaman Lafiya Ya Qare Daga Ranar, Firgici, Dimauta, Razani, Bakin ciki, Faduwar Gaba, Mafarki Maras Dadi Sune Abokan Tarayyar Zuciyata. Ina Qaunarki ne Daga Qoqon Raina. Ki Kula Dani Masoyiyata.
.

Daya Daga Cikin Alamun Soyayya ta agateki Shine Na Nuna kishina Akanki. Wannan Yasa Bana Qaunar Naga Wani Ya Kusanci inda Kike, Banason Komai Ya Hadaki Da Wanin da ba Muharramin ki Ba. HubbyNa Inason Ki Kasance Cikin Farin ciki Tare Dani Muyi Aure Mu Morewa Rayuwarmu. Shine fatana.

Dake Na Fara Kuma Dake Zan Gama Rayuwata Isha Allahu. Sabon Littafi Zan Bude Mana Na Soyayya. Sirrin Zuciyata Ke Zan Bayyanawa, Komai Nawa Naki ne Ba Abinda Zan Ware. Kece Fitilar rayuwata, Kece Jigon Rayuwata Ki Rike Wannan Matsayin Dana Baki Ki Tabbatar Kin mulkeshi Yadda Ya Kamata Kuma Yadda nakeso.
Tinanin Ki Yana Zuwamin Ne a Lokacin dana tina ki, Nakan Tinaki Alokacin dana Ke Halin Kadaici, shikuma Kadaici Ya zama Min Kamar Karfen Qafa. Domin Muddin Bakya Cikin rayuwata To Nida Kadaici Rabuwarmu Sai Mutuwa. Idan Na Kalli Tafiyarki Sai Naji Inama Ni kike yiwa. Idan Naga Fuskarki Sai Nace Yaushe Zan Mallaketa, Idan Naji Muryarki Me zaqin Nan, sai Naji inason Na Ringa Sauraron Ta, Yayin Da Take Tadani Daga Bacci. Ina Kallon Fuskarki Me Hade Da Murmushi Yayinda Muke karin Kumallon Safe, Kyakkyawan Bakin ki mai Hade Da Kyawawan Hakora A jere Tamkar Zinare sumin Kisss, wayyo ji Zanyi kamar Bana Duniyar.

.

Kinada kima A idanuna shiyasa bana iya dadewa ina kallon tsakiyar Idanuwanki.


Chikakkiyar gaisuwa, tareda budewar dukkan wasu kofofin farin ciki zuwa gareki Abar kwatancena. Idan gaisuwa ta kammala sai na wuce zuwa aiken da zuciyata tayi min mai dauke da sakonnin Qaunarki


Ya zama Dole Insamu Nutsuwa, Domin In Gabatar Da Natsattsen Sakona Zuwa Gareki Ma'abociyar Nutsuwa Da Fahimta


Dukkan wasu lafuzzan kaunata ina gabatar dasu agareki domin kece kikai awon gaba da Tunanina


Burin Zuciyata ki zauna cikin Qoshin lafiya ki taka lafiya ki sauQa lafiya kija ragamar mulkin zuciyata cikin koshin Lafiya Da Shauki.

Kece Kika Zamo Silar Tsamoni Daga Fadawa Cikin Ambaliyar Rudewar Rashin Tabbacin Zaman Lafiyar Zuciyata

Ina kara sanar dake cewa kece kadai na mikawa dukkan zuciyata domin ki shayar da ita madarar Zumar_Kaunarki

Na Sadaukar Miki Da Duk Farin Cikina. Fatana Akoda Yaushe Ki Kasance Acikin Yanayi Mai Dadin Dake Dadada Ruhi.

..........Suna....... Inajin cewa na samu komai a rayuwa, amma Akwai Abunda nake da gurbin sa, kuma inajin Cewa Kece Zaki cikamin Wannan Gurbin, idan muka ga wasu mutanen Sai muji muna son bin bayansu, kadan daga ciki kuma Sai muji munason hada tafiya dasu, amma ke kawai sai naji inasone na rike hannunki mu tafi, Banason Rasaki a rayuwata Domin inasonki ne na har abadan abada. Kuma har izuwa gaba da numfashina mutuwa ma saidai ta dauki ruhin mu, amma ko bayan mutuwa sai Munyi rayuwa dake, Duk tsawon lokacin dana dauka dake ban taba yin Asara ba duk abunda nake miki ribace agaremu ni dake. 

.

Zan Fi Kowa Dacewa Idan Kika Rike Kaunar Da Ke Tsakaninmu Nai Maki Wani Tanadi Duk Sanda Kika Kasance Uwar ‘Ya’yan Mu Zuciyata Za Ta Kasance Mai Yabonki Da Kuma Nuna Maki Kulawa Wanda Uwa Take Bawa Danta, Ki Kasance Tawa Ta Har Abada. Idan Kowa Haka Ta Samu A Tsakaninmu Ba Abin Da Za Mu Nema A Cikin Wnnan Duniyar Saboda Ya Cika Mana Burin Mu Sai Dai Fatan Mugama Da Dunia Lafiya

.

Inuwarki Zata Min Dadi Farinkiciki Ki Zai Kayatar Dani, Rayuwarki Zata Amfanar Dani. Xuciyar Ki Zata Mini Rana, Kalaman Ki Zasu Min Magani, Tafiyarki Zata Debe Min Kewa, Murmushin Ki Zai Sani Farin Ciki. Ina Son Abunda Kike So Bana Qaunar Abunda Bakya So, Ina Son Me Sonki Amma Bada Soyayya Ba, Ina Kishi Akanki Sosai Bana Son Koda Quda Ya Taba Ki Bada Hakki Ba, Ko Kallon Banza Banso Naji Za’a Miki Bale Ma A Miki, Rayuwata Zata Cika In Dake. Ina Qaunar Ki.
 
 
 


 
 

Zan Kasance Da Kullum Da Handkerchief Akoda Yafe Ina Yawo Dashi Dauke Da Tambarin Soyayyar Ki, Domin Kada Kiyi Kuka Na Kasa Share Miki Hawaye, Ina Qaunar Smile A Face Dinki Koda Tuntube Kikai To Lallai Raina Zai Ciwo, A Karkashin Mulkina Kina Da Duk Wani Jindadi Da Mace Take Nema A Wurin Miji.

.

Aminci Da Yarda Ya Qara Tabbata Ga Mamallakiyar Zuciyata, Farin Wata Mai Haskaka Zuciyata, Kece Kika Zamo Farin Cikin Rayuwata, Ina Da Tabbacin Cewa Zuciyarki Tana Cike Da So Na Da Shauk’ina Had’i Da Bege Na Acikin Wannan Sansanyar Safiyar Kamar Yanda Tawa Ta Kasance Haka, Zai Zama Abin Alfaharina Cewa Wannan Sak’on Nawa Shine Abu Mafi Soyuwa Daya Fara Riskarki Cikin Wannan Ni’imtacciyar Safiyar Masoyiyata, Aminiyata Abokiyata. Shalele Na. 

.

Godiyta Tayi Alkawarin Riskar Ki A Kowani Lokaci. Domin Nuna Karramawa Agareki, Rarrashina Zai Kasnce Dake Aduk Lokacin Da Kike Tare Dani. Lafiyata Itace Samun Naki Lafiyar, Idan Nai Farin Ciki Murmushinki Na Hango.


A Duk Inda Kika Je Ki Tabbatar Da Cewa Ina Biye Da Ke, Ko Da Ban Zo A Zahiri Ba To Kuwa Zan Zo Miki A Cikin Bacci, Ke Ma Za Ki Bayyana A Cikin Mafarki Na, Mu Kasance A Tare Da Juna, Cikin Wani Lambu Mai Cike Da Furanni Mabambanta Launi. Begenki Shi Ne Abun Yina A Kullum.

.

Lallai Ke Din Ta Daban Ce, Kina Da Wata Baiwa Wadda Ba Kowa Ne Zai Gane Hakan Ba, Daga Ciki Akwai Ta Zazzakar Murya Da Tattausan Murmushi. A Lokuta Da Yawa, Kalmomi Sukan Gagari Furtawa, Domin Bayyanar Miki Da Adadin Yadda Sonki Yake Kara Mamaye Zuciya Ta A Kullum. Bana Fatan Zuwan Ranar Da Zan Gaza Wajen Nemo Kalmomin Da Zan Furta Miki Cewa INA SON KI. Ganin Yau Ya Sani Fari Ciki Sosai I Love You
Daya Daga Cikin Abun Dake Zuciyata Shine Tinanin Ki, Tinanin Ki Ya Min Sarqa Ya Zarge Ni Nishi Nake Amma Dakyar Nake Numfashi. Na Biyu Shine Qaunar Ki, Qaunar Ki Tazo Tana Hiranta Min Cewa Idan Har Na Kuskura Na Rasaki Amatsayin Mata To Zata Iya Yin Ajalina Dakyar Na Bata Hakuri Nace Mata Ina Qaunar Ki.

.

Alkawari Ne Na Dauka, Ba Zan Taba Barin Damuwa Ta Wanzu A Cikin Zuciyar Ki Ba Matukar Muna A Tare Da Juna, Ina Fatan Nan Da Wani Dan Lokaci Ki Tabbatar Da Hakan Bayan Kin Zamo Mata A Gare Ni, Ke Kadai Zuciyata Ta Amincewa, Ki Huta Lafiya. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son Ki.

.

A Cikin Dukkan Mafarkan Da Nake Yi Bayan Haduwata Da Ke, Ban Taba Ganin Wata Rana Da Ta Zo Ta Kuma Wuce Ba Tare Da Na Gammu Tare A Cikin Lambu Mai Sanyaya Zuciyar Masoya Ba, Rayuwa Ce Mai Dadi Ke Gudana A Tsakanin Mu, Ina Fatan Wannan Rana Ta Bayyana A Gare Ni A Zahiri Ba A Cikin Mafarki Ba Kawai. 

.

Tabbas Nasani Cewa Ban Kasance Farkoba Ban Kuma Zamo Karshan Furta Kalmar So Agarekiba Iyayen Ki Su Suka Fara. Amma Kuwa Zuciya Da Marari Ba’a Hanata Abinda Take Kauna Wanda Koda An Haneta Hakurinta Bai Wuce Kaddaraba. Har A Kullum Bakina Ya Saba Furta Kalmar So Agareki Wanda Ban Taba Canza Batuna Akan Hakan Domin Baiyanarki Ta Kasance Tamkar Fitowar Hasken Rana A Kowanne Lokaci Wanda Ganina Baya Samuwa Sai Dashi Hakan Yasa Nake Kallanki A Matsayin Jagora Wacce Zuciya Ta Kasance Mai Yin Alfahari Sannan Ta Amintarwa Kanta Zabi Mafi Dacewa Agareta.


KALAMAN SOYAYYAAminchin Allah Ya Qaratabbata Agareka Ya Kai Ma.Abocinrayuwata.Kaxamto Wata Nikuma Naxamto Xara Muhadu Mubada Haske.Kaxam To Ni Inxamto Kai Muhadu Mubawa Maqiya Kunya.Kaxamto Nono Inxamto Dambu Muhadu Muhana Maqiyammusha. Ina Sonka Xan Aureka Matuqar Inaraye Da Ixinin Allah Idam Harhaka Ta Faru To Lallai Xakasha Madararso Xallar Na Soyayya Basurki. Idan Na Aureka Xakasha Mamaki Insha Allah Kai Dai Muyi Fatan Allah Yakai Mu Lokacin.

.

Har A Kullum Bakina Ya Saba Furta Kalmar So Agareki Wanda Ban Taba Canza Batuna Akan Hakan Domin Baiyanarki Ta Kasance Tamkar Fitowar Hasken Rana A Kowanne Lokaci Wanda Ganina Baya Samuwa Sai Dashi Hakan Yasa Nake Kallanki A Matsayin Jagora Wacce Zuciya Ta Kasance Mai Yin Alfahari Sannan Ta Amintarwa Kanta Zabi Mafi Dacewa Agareta.Lokachi NE Ya Sanyoki Cikin Rayuwata Batareda Ni Dake Mun Taba Tsammanin Faruwar Hakan Ba,Yau Da Gobe Kuma Ta Baiwa Soyayyarki Damar Samun Sassaukar Doguwar Hanya Wadda Ke Zuwa Har Cikin Fadar Zuciya A Dan Karamin Lokachi,Ni Kuma Na Soki Fiyeda Duk Wani SO Danayi A Shekarun Baya,Wadannan Sune Dalilan Da Suka Sa Kikayi Zarra A Wajena,Me Xai Hana Zucia Tunowa Dake A Duk Lokacin Da Aka Ambaci Sunanki Koda Bake Ake Nufi Ba,Idan Har Mutumin Dake Dauke Da Kudi A Aljihunsa Zai Tuna Dasu Duk Bayan Yan Sakanni,Ni Me Zai Hana In Tuno Dake A Matsayinki Na Wadda Tsallake Aljihu Na Sakata A ZUCIA, Kuma I Love You.

.

Duk Da Ya Kasance Nida Ke Muna Nesa Da Juna Hakan Baya Hanani Tunaninki Hakan Baya Hanani Kaunarki Kin Zamo Ta Musamman Daga Cikin Mutane Na Musamman Da Na Ta6a Haduwa Da Su A Rayuwata, Kin Shiga Zuciyata Kin Zauna Ta Yadda Ba Zan Iya Mantawa Da Ke Ba Har Abada. Ina Fata Da Burin Kasancewarmu Tare A Daula Mafi Tsari Da Kyawun Burgewa Wato Aljanna. Cikin Nishadi Da Yalwatuwar Murmushin Fuska Nake Mai Furta Miki Cewa Ko Mutuwa Ta Rabamu Zamu Hadu A Aljanna Insha Allahu.

 
 


 
 

Zan Kula Dake Zan Baki Duk Wani Jin Dadi Da Mace Ke Nema Wurin Mijinta, Kuma Ina Fata Da Rokon Allah Yasa Na Iya Baki Duk Abunda Kike Bukata, Ina Sonki Sosai Fiye Da Dukkan Abunda Na Mallaka, Idan Banyi Rayuwata Dake Ba Bansan Yadda Zan Kasance Ba, Idan Ina Tina Ki Ji Nake Na Qagu Da Inga Na Mallakeki Na Ganki Cikin Inuwata Kiyi Frin Ciki Sanadiya Ta, Qaunar Nake Sosai

.

Haruffan Da Nayi Amfani Dasu Wajen Rubuto Maki Sakon Nan Ba Zasu Iya Nuna Maki Hoton Abinda Nake Son Sanar Dake Ba,Amma Zasu Kwatanta Maki Irin Yadda Abin Yake A Chikin Raina, ZUCIYATA Itace Babbar Igiyar Dake Juya Akalar Ruhina Da Gangar Jikina,SO DA KAUNA Yasa Nake Son In Zabeki Ki Zama Babbar Yar Majalisar Fadar Zuciya Wadda Zata Juya Akalata Da Zuciyar Tawa Gabadayanmu, Ni Kamar Maharbi NE Sakona Kuma Tamkar Kibiya CE A Hannuna Nayi Saitin Zuciyarki Irin Saitin Da Bani Tsammanin Zan Kuskure,Idan Har Ban Samu Ba Ina Fata Zaki Dubeni Da Idanun Tausayi Ki Qara Damke Soyayyata, I Love You

.

Bakina Yana Matukar Son Sanar Dake Irin Yadda Nake Sonki, Kunnena Kuma Yana Yana Jin Dadin Sauraren Sassanyan Sautin Siririyar Muryarki, Idona Kuma Kece Wadda Yafi Bukatar Gani A Kullum,INA SONKI Fiye Da Yadda Zan Jaraba Fasalta Maki Kuma Fiyeda Yadda Kema Zakiyi Hasashen Irin Girman Son,Ki Bani Dama In Zama Sashe Na Musamman Na Rayuwarki Mai Karfin Fada Aji A Cikin Fadar Zuciya,Har Wata Rana Siffar Fuskokinmu Ta Zama Kala Daya,Kada Kiji Tsoron Komai Game Dani Nayi Maki Alkawarin Soyayyata A Yanzu Da Muke Matsayin SAURAYI DA BUDURWA,Da Kuma Lokachin Da Zamu Zama MIJI DA MATA, Har Mu Koma TSOHO DA TSOHUWA, Zw Kushewar Mu. Kece Ki Kasance Uwargida A Gidana Na Duniya Da Kuma A Aljanna Musha Soyayya Muyi Rayuwar Da Ba Tinanin Mutuwa Ko Ciwon Ciki.


Na Za6eki Fiye Da Mallakar Komi Na Rayuwa Tamkar Shigar Lafiya Acikin Jikina. Na Nisanta A Cikin Sonki Da Kaunarki Ta Yadda Ba Mai Iya Hange Bare A Sami Kamata Domin Ni Agareki Na Kusantar Da Zuciyata. Na Kanyi Farin Ciki Da Abinda Soyayya Ta Samar Agareni Dadi Ko Wuya Musamman A Dangane Soyayyarki Badan Komiba Sai Dan Na Bayyana Sirrina Agareki Saboda Ke Ce Abin Da Rai Da Zuciya Suka Zamto Zabin Ta Domin Ki Zamo Abokiyar Rayuwar Ta. Ina Sonki Abune Wanda Baki Ya Saba Furtawa Akoda Yaushe Amma Nasarar Soyayyarki Gareni A Kullum Shine Ki Kasance A Matsayin Matar Aurena.

.

Zanso Ki Isarmin Da Wannan Sako Nawa Zuwa Ga Zuciyarki. Cikin Ko Wanne Lokaci Nakan Zamo Mai Nutsuwa A Duk Sanda Idanuwana Ke Tozali Ga Kyakkyawar Fuskarki. Ke Na Rika A Cikin Raina Da Sonki Nake Kwana Da Kaunarki Na Tashi. Sonki Halittane Dashi Nake Rayuwa A Jikina Dukkan Farin Cikin Zuciya Gareki Nake Samu. Ki Soni Domin Allah Kece Zabi Na Zuciyata Rayuwata Dake Ta Dace. 

.

Cikin Yan Kwanakin Nan Inajin Shauki A Zuciyata Yana Qaruwa Fiye Da Ko Yaushe. Soyayyar ki tana qaruwa Inajin Qaruwar kusancina Dake ta jini, Tabbas a jinina Nakejin Qaunarki. Inason Tsakanina Dake Mu Rinka Mutunta Junan mu. Mu Girmama Junan Mu. Mu Yiwa Junan Mu Duk Abunda Mukeso Kada Mu Sabawa Junan Mu. Idan Har Munason Qaunar Da mukewa Juna ta wanzu zuwa lokacin da muke Bukata To Sai Mun Girmama Soyayyar mu, har Yanxu na Kasa Yimiki Kishiya a Cikin Xuciyata Saboda Na Yarda Dake Sosai Fiye da Yadda kike Tsammani. Yadda Nakeji akanki Bana Iya Zayyanashi Kuma A jikina Nakeji yana Min Yawo. Ko Mutuwa Banason Ta Rabani Dake Wlh. Bakina ba zai Iya Furta Yadda zuciyata Take Jinki Ba. Kawai Hakuri Nake Na Danne, Kalamankine Kawai Suke Iya Min Magani.


.

Thank you for your message.

Previous Post Next Post