ABUBUWAN DA MATA SUKA TSANA

 ABUBUWAN DA YAN MATA SUKA TSANA
YAN SAMARI SAI A KIYAYE DAN QARA DANQO SOYAYYA.

 

 Kada Ku Manta Kuyi Download na Application Namu domin kuna samun Sabbin Posting Namu Akan Lokaci👇🏻  

 KALAMAN SOYAYYA APP 



1. kasani aboki ƴan mata basa son yawan tambaya ta ƙwaƙƙwafi nasa suji aransu kamar zarginsu kake, amma ka iya tambaya me Sauƙi misali jiya nazo bakyanan masoyiya ina kikaje ne? Sai tace ma wlh gu kaza naje, to kacemata to dafatan kindawo lafiya dai tawan kana murmushi alamar baka damuba amma kar ka sake tambayarta mekikayi, ke dawa kuka je, to ya akai baki dawo da wuriba meyasa baki bar sallahu ba da sauran su, suna jin haushi sosai, kuma basajin dadin hira da irin waɗannan samarin.

Karanta: LAIFIN MAZA DA MATA ACIKIN SOYAYYA

2. kada ka yabi wata budurwa ko mata ko yar uwarkace agaban budurwarka, mata nada saurin kishi da zargin namiji akan wata budurwa koda sunsan yar uwarkace.



 Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE



3. kada ka bawa budurwar ka labarin tsohuwar budurwarka da yadda kukai soyayya da ita koda ita tanema kabata sama sama.

4. kada kana hira da budurwarka, kafiye kalle kalle, ko kallon wata wacce tazo wucewa ka bar fuskantar budurwarka.


Karanta:  YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA



5. Kada ka yawaita kallon jikin budurwarka wato daga ƙasanta zuwa sama, hakan nasa su jin kunya da wani abu azuciyarsu kuma basu fiya son hakan ba a kowanne lokaci, yadda akeso kayi shine ka kalli fuskarta da idanunta hade da murmushi, wannan sunsan kallone na so tuni zasuyima dariya dawani irin kallo me rikita masoyi wanda bai fi second dayaba, kaji saboda tayi farinciki tarasa mezatace sai kaji tace to meye? Ko umm ni kadena kallona tana murmushi irin wannan shi mata keso, bawai kana kallon halittar jikintaba aboki.


 Karanta: YADDA SAMARIN DA SUKA FI SAMARIN YANXU IYA SOYAYYA


6. Yanga da gwalli, ɗaukar kai girman kai da iyayi. dukka mata sun tsani wannan dan suna gani yanga da gwalli da iyayi da daukar kai duk sufface tasu ta mata toyaya kaikuma zaka ara ka yafa.

7. Watsarwa yayin hira.
8. lalaci da sonjiki mata basa son lazy.

9. Sa ido mata basa son sa ido.
10. Zargi

 

 Karanta: SIRRINKA 21 DAKE SAKA SOYAYYA JIMAWA


11. Aikata ayyukan masha ah kamar sata, fada, shaye-shaye mata sun tsani halayennan. Aboki kasani mata sun tsani dabi u dayawa, wasu dabi'un damaza suke so, sukuma haka mata sun tsane su, haka kuma wasu dabi'un da mata keso suma maza sun tsani wasu.
Saboda haka kayi ƙoƙari kagane me budurwarka take so da wanda bata so.

 

 Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA



* matuƙar baka iya rarrashin budurwa ba!
* Baka san me take so ba!
* Baka san me ta tsana ba!

To bazaka taba yin soyayya me dadi ba, saidai kullun cikin faɗa, zargi, damuwa, tunani, kiyi haƙuri, kiran aboki yai muku sulhu kuma ko kunyi aure ma haka zaku sami matsala.

Allah ya ƙara danƙon soyayya har ayi aure ƴan samari asamar da zuriya tagari.

1 Comments

Thank you for your message.

Previous Post Next Post