ABUBUWAN DA MATA SUKA TSANA

 ABUBUWAN DA YAN MATA SUKA TSANA
YAN SAMARI SAI A KIYAYE DAN QARA DANQO SOYAYYA.

 

 Kada Ku Manta Kuyi Download na Application Namu domin kuna samun Sabbin Posting Namu Akan Lokaci👇🏻  

 KALAMAN SOYAYYA APP 



1. kasani aboki ƴan mata basa son yawan tambaya ta ƙwaƙƙwafi nasa suji aransu kamar zarginsu kake, amma ka iya tambaya me Sauƙi misali jiya nazo bakyanan masoyiya ina kikaje ne? Sai tace ma wlh gu kaza naje, to kacemata to dafatan kindawo lafiya dai tawan kana murmushi alamar baka damuba amma kar ka sake tambayarta mekikayi, ke dawa kuka je, to ya akai baki dawo da wuriba meyasa baki bar sallahu ba da sauran su, suna jin haushi sosai, kuma basajin dadin hira da irin waɗannan samarin.

Karanta: LAIFIN MAZA DA MATA ACIKIN SOYAYYA

2. kada ka yabi wata budurwa ko mata ko yar uwarkace agaban budurwarka, mata nada saurin kishi da zargin namiji akan wata budurwa koda sunsan yar uwarkace.



 Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE



3. kada ka bawa budurwar ka labarin tsohuwar budurwarka da yadda kukai soyayya da ita koda ita tanema kabata sama sama.

4. kada kana hira da budurwarka, kafiye kalle kalle, ko kallon wata wacce tazo wucewa ka bar fuskantar budurwarka.

Karanta:  YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA 

5. Kada ka yawaita kallon jikin budurwarka wato daga ƙasanta zuwa sama, hakan nasa su jin kunya da wani abu azuciyarsu kuma basu fiya son hakan ba a kowanne lokaci, yadda akeso kayi shine ka kalli fuskarta da idanunta hade da murmushi, wannan sunsan kallone na so tuni zasuyima dariya dawani irin kallo me rikita masoyi wanda bai fi second dayaba, kaji saboda tayi farinciki tarasa mezatace sai kaji tace to meye? Ko umm ni kadena kallona tana murmushi irin wannan shi mata keso, bawai kana kallon halittar jikintaba aboki.

 Karanta: YADDA SAMARIN DA SUKA FI SAMARIN YANXU IYA SOYAYYA 

6. Yanga da gwalli, ɗaukar kai girman kai da iyayi. dukka mata sun tsani wannan dan suna gani yanga da gwalli da iyayi da daukar kai duk sufface tasu ta mata toyaya kaikuma zaka ara ka yafa.

7. Watsarwa yayin hira.
8. lalaci da sonjiki mata basa son lazy.

9. Sa ido mata basa son sa ido.
10. Zargi

 Karanta: SIRRINKA 21 DAKE SAKA SOYAYYA JIMAWA 

11. Aikata ayyukan masha ah kamar sata, fada, shaye-shaye mata sun tsani halayennan. Aboki kasani mata sun tsani dabi u dayawa, wasu dabi'un damaza suke so, sukuma haka mata sun tsane su, haka kuma wasu dabi'un da mata keso suma maza sun tsani wasu.
Saboda haka kayi ƙoƙari kagane me budurwarka take so da wanda bata so.

 Karanta: SIFFOFIN SAMARI MAYAUDARA 


* matuƙar baka iya rarrashin budurwa ba!
* Baka san me take so ba!
* Baka san me ta tsana ba!

To bazaka taba yin soyayya me dadi ba, saidai kullun cikin faɗa, zargi, damuwa, tunani, kiyi haƙuri, kiran aboki yai muku sulhu kuma ko kunyi aure ma haka zaku sami matsala.

Allah ya ƙara danƙon soyayya har ayi aure ƴan samari asamar da zuriya tagari.

 ABUBUWAN DA SUKE BATA SOYAYYA.  

Bayanine akan wasu halaye dasuke janyowa soyayya matsala ko batashi.  

1. Ruwan ido 

2. Ƙarya 

3. Munafurci 

4. Son abun duniya. 

5. Zargi  


Kada Ku Manta Kuyi Download na Application Namu domin kuna samun Sabbin Posting Namu Akan Lokaci👇🏻   

KALAMAN SOYAYYA APP 

 

Karanta: HALAYEN-MATA-TA-GARI

 

1. RUWAN IDO yana da matuƙar kawo matsala a soyayya, sai kaga budurwa ta tara samari samada 5 ta kasa zabar ɗaya, a ƙarshe ta zabi wanda ba nagari ba. RUWAN IDO KANSA AYIMIKIKI ZARGIN KE YAR ISKACE DAN KINA TARA SAMARI SUNAI MIKI LAYI.  ZAIKUMA SA KI KIYI SAKE RESHE KAMA GANYE, DA RAGE MIKI ƘIMA KEDA IYAYENKI.  


Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA

 

2. ƘARYA.  KOWA YASAN ƘARYA A SOYAYYA, IMMA SAURAYI YAYIWA BUDURWA ƘARYA DON YA MALLAKE TA, KO ITA TAYIWA SAURAYI ƘARYAR ABU kaza da kaza kamar, babban gida, mota, kudi, matsayi da sauran su alahali BABU, KO ITA TAYI MASA ƘARYAN ITA YAR WANI CE ALHALIN KUMA ƘARYA TAKE .  IN ANA ƘARYA A SOYAYYA ZA A IYA FUSKANTAR WADANNAN MATSALOLIN.  

*Samari Su Tsaneki 

*Ki zama Marar Daraja 

*Ki zama Cikin Ɗimuwa Dan Za A Ƙureki Wataran Kiji Kunya 

*Mayaudara Na Iya Zuwa Gunki Har Su Yaudareki. 

*Ƙawaye Sunai Miki Kallon Banza. 

*Ƙin yarda Da Masoyi Komasoyiya

Karanta: DABARU 15 DA MAZA KE AMFANI DASU 

3. MUNAFURCI. Shine boyewa masoyi ko masoyiya haƙiƙanin abun dake rai, kamar kana ce mata ita kadaice budurwarka amma kuma ashe kana da wata koma wasu, idan tagane zata ɗauke ka munafuki dan tasan waccar ma haka kake ce mata .  

*MUNAFURCI NASA RASHIN YARDA A TSAKANIN MASOYA, DA YAWAN FAƊA, DA ZARGI, KUMA KO DA KIN FADƊI KO KA FAƊI GASKIYA BAZA'A YARDA BA A WASU LOKUTAN. 

*NASA AYI BAYA-BAYA DA MASOYI KO SA SHAKKU A SOYAYYA, DA RAGE DARAJAR MASOYI. 

 Karanta: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA 

4. SON ABUN DUNIYA:

shine budurwa tana miƙawa saurayinta buƙatunta da matsallolinta na rayuwa dan yabata wani abu ko yai mata maganin su. takowacce hanya. Musali. Nunamasa afili yasai miki mota, waya babba, kayan kwalliya da sauransu.  Son abunduniya nasa 

* Ayi miki kallon yar iskace koda bahakabane  

* Cikin sauƙi masu bata ƴanmata na iya yaudararki da abunduniya su bataki.  

*Rashin aji da ƙima agun samari da rasa samari nagari. dan tsanarki za ayi. Kowa yana tsoran zuwa gunki dan dayazo za kifara yimasa tallan buƙatunki, sayamin kaz, yimin ankon wance, cikamin kudi nasai waya da dai sauransu  

Karanta: ABUBUWAN-DA-YAKAMATA-KA-SANI-RAYUWA 

4. ZARGI Zargi shine yawan zato ga masoyi akan abunda ba'a da tabbas. ZARGI NA BATA SOYAYYA DUKA KODA ANYI AURE. nasa ƙin Amincewa da juna da yawan fada da sauransu. Dan haka, ƴan uwa da samari ingantacciyar soyayya dolene a cire wadannan halayen marasa kyau a soyayya. abmaye gurbinsu da dabi'u masu kyau kamar su gaskiya, Ruƙon amana tausayi, haquri da juriya da sauaransu.

  ALLAH YABAMU MASOYA NAGARI


1 Comments

Thank you for your message.

Previous Post Next Post